Fani-Kayode ya nemi sauki a Kotu

Fani-Kayode ya nemi sauki a Kotu

– EFCC tana zargin Fani-Kayode da laifin karban kudi daga hannun Dasuki

– Hukumar EFCC tace Fani-Kayode ya ci kudin makamai

– Fani-Kayode ya nemi a sasanta a wajen Kotu

Fani-Kayode ya nemi sauki a Kotu

Fani-Kayode ya nemi sauki a Kotu

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tana zargin wani tsohon Minista a lokacin shugaba Olusegun Obasanjo kuma na gaban-goshin Jonathan da laifin cin hanci da rashawa. Ana zargin Femi Fani-Kayode da yin gaba da wasu Naira Miliyan 26.

Sai dai Fani-Kayode ya nemi Hukumar EFCC ta sassauta masa a sasanta ba tare da an shiga dakin Kotu ba. Kayode yace ta bakin Lauyan sa Ahmed Raji, tun da kudin ba masu yawa bane gara ayi magana kafin a kai ga Kotu.

KU KARANTA: Ba na tsoron Buhari -Inji Fayose

Ana zargin Fani-Kayode da karbar wasu kudi lokacin yakin neman zaben shugaba Jonathan shekaru biyu da suka wuce daga hannun Sambo Dasuki wanda ya rike ofishin mai ba shugaban kasa shawara game da harkar tsaro.

Kwanan kuma dai Hukumar ta EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamna Isa Yuguda da ke Unguwar GRA na Bauchi. Wani Jami’in Hukumar EFCC yace za a rike gidan ne na wani dan lokaci kafin a kammala bincike.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel