Babu abunda zai dakatar da Arewa da Buhari a 2019 – Sani

Babu abunda zai dakatar da Arewa da Buhari a 2019 – Sani

- Tsere don zaben shugabancin kasa na 2019 ya fara kafuwa

- Shugabanni da daman a ta bayar da ra’ayinsu a kan al’amarin

- Wani tsohon kakakin kungiyar Arewa, Anthony Sani ya shiga sahun muhawaran

Wani sakataren labarai na kungiyar Arewa ta kasa, Mista Anthony Sani ya fadi zuciyarsa a kan zaben shugabanci na 2019 a Najeriya.

Babu abunda zai dakatar da Arewa da Buhari a 2019 – Sani

Da yake magana tare da Leadership a jihar Kaduna a karshen mako Sani ya kaddamar da cewa babu abunda zai dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da arewa shugabantar kasar karo na biyu a zaben 2019.

Sani ya bayyana cewa idan yan Najeriya suka zabi wani dan takara mai rauni a kan mutun mai karfi kamar Buhari wadda ke aiki a karkashin yanayi mafi wahala, Najeriya zata durkushe.

KU KARANTA KUMA: Cutar dake damun shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ya kara da cewa kirkiro sabon jam’iyya da yan siyasa keyi bazai kayar da mulki ba kamar yadda yan Najeriya da dama sunfi son Buhari fiye da ko wani mutun.

Sani, wanda ya kasance kakakin tawagar Arewa a shekarar 2014, yace koda dai Buhari na da lokacin sa, shine zabi mafi inganci ga Najeriya.

Ya soki wasu hasasshe da fastoci sukayi a kan gwamnati mai ci, cewa fastocin haya ne ke haka don gwada ra’ayin yan Najeriya kan wadanda ke son tsayawa takarar shugabanci nan gaba.

Sani yace Buhari zai gama shekarunsa takwas a kan mulki kamar yadda yan Najeriya da dama sun fi son sa a kan wani mutun ya kuma kara da cewa arewa bata da wani dan takara da yafi Buhari a yanzu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel