Cameroon ta lashe kofin Afirka

Cameroon ta lashe kofin Afirka

- Kasar Kamaru ta lashe gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a karo na biyar bayan ta doke Masar da ci 2-1

- Vincent Aboubakar, wanda aka sako daga baya ne ya zura kwallon da ta ba su nasara minti biyu kafin a tashi daga wasan

Cameroon ta lashe kofin Afirka

Cameroon ta lashe kofin Afirka

Tun da farko sai da dan wasan Kamaru Nicolas Nkoulou ya farke kwallon da Masar ta ci su, abin da ya bai wa 'yan wasan kwarin gwiwa.

A wani labarin kuma, Barcelona ta doke Atletico Madrid a karawarsu ta farko ta wasan kusa da na karshe na cin kofin Copa del Rey a gidan 'yan Madrid din Vicente Calderon.

Luis Suarez ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na bakwai da shiga fili, sannan kuma Lionel Messi ya kara ta biyu a minti na 33.

Sai dai Antoine Griezmann ya ba wa masu masaukin bakin kwarin guiwa a karo na biyu da za su yi a ranar Talata a Nou Camp, sakamakon kwallo daya da ya rama a minti na 59, wadda ya ci da kai.

Alaves da Celta Vigo su ne sauran kungiyoyin da suka kai wasan na kusa da karshe, inda za su yi wasansu na farko ranar Alhamis.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel