Laftanar janar Tukur Buratai ya baiwa yan banga kyautan N1m

Laftanar janar Tukur Buratai ya baiwa yan banga kyautan N1m

Babban kwamandan hafsoshi da mayakan rundunuar sojan kasa Laftanar janar Tukur Buratai ya baiwa yan kungiyar mafarauta da yan banga tallafin naira miliyan daya dake karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi don siyan kayan aiki.

Laftanar janar Tukur Buratai ya baiwa yan banga kyautan N1m

Laftanar janar Tukur Buratai

Kwamandan Birget ta 33 na rundunar sojan kasa dake Bauchi Brigediya A.I Dusu ne ya mika musu kudaden a ranar Lahadi 5 ga watan Feburairu a garin Darazo a madadin Janar Buratai.

A.I Dusu yace Buratai ya yaba da kokarin da yan bangan tare da mafarautan ke yi wajen goyon baya tare da agaza ma sojoji wajen a yaki da sukeyi da yan Boko Haram da masu aikata miyagun laifuka.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano zata dauki malamai 2,000 aiki

Laftanar janar Tukur Buratai ya baiwa yan banga kyautan N1m

yan banga

Sa’annan ya jinjina ma kwamitin tsaro na karamar hukumar tare da al’ummar yankin saboda jajircewarsu da tabbatar da ganin sun samar da tsaro a yankinsu, inda ya shawarce su dasu cigaba da yin hakan.

Shima shugaban riko na karamar hukumar Darazo Alhaji Baba Danlawan Hamza ya nuna farin cikinsa dangane da tallafin da Buratai ya baiwa yan bangan, inda yace hakan na nuni da cewar ana sane da kokarin da suke yi, kuma ana godiya.

Shugaban na riko ya bada tabbacin karamar hukumarsa zata cigaba da taimaka ma yankato dagora tare da mafarautan don samun daman kara kokari a taimakon da suke baiwa jami’an tsaro. Daga karshe Hamza ya yaba ma shugabancin jam’iyyar APC tun daga shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa gwamnan jihar saboda damuwa da sukayi da matsalolin tsaro.

Yayin da yake nasa bayanin a madadin matasan, Alhaji Abdu Latus ya gode ma rundunar sojan kasa sakamakon halin kirkin da suka nuna musu, kuma ya tabbatar musu zasu kara kokari fiye da yadda suke yi a baya.

Shima hakimin Darazo ALhaji Bababa Ibrahim yayi alkawarin fadakar da mutanensa wajen ganin sun cigaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya don kare lafiyarsu da dukiyoyinsu, sa’annan ya shawarce su su zauna lafiya da juna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel