An kama mafarauci cikin daji tsirara tare da matar aure a jihar Delta

An kama mafarauci cikin daji tsirara tare da matar aure a jihar Delta

An kama matar aure mai shekaru 43 tana bacci tare da mafarauci a wani daji, a Asaba jihar Delta.

An kama mafarauci cikin daji tsirara tare da matar aure a jihar Delta

An kama mafarauci cikin daji tsirara tare da matar aure a jihar Delta

Anga matar wacce aka kira a matsayin Dumebi a cikin wani kurmin daji a Ugholu tsirara tare da mafaraucin.

An tattaro cewa a koda yaushe Dumebi na daidaita mijinta da mafaraucin. A koda yaushe Dumebi na wasa cewa mijinta malalaci ne ba kamar mafaraucin ba wanda a kullun yake kashe dabbobi.

KU KARANTA KUMA: Kotun Amurka ta dakatar da dokar Trump na hana musulmai shiga kasar

Wani dan kungiyar banga na Ugholu, Sunday Igbokwe, wanda ya kama mutanen biyu suna aikata masha’a ya bayyana cewa sun shiga dajin ne bayan matar mafaraucin ta tafi kasuwa.

Dattawan garin Ugbolu sun kori mafarucin wanda ya yarda da cewan ya kwanta da matar auren. A cewar wani dattijo, Cif Joseph Agbereh, an kori mafaraucin ne kan zargin ya kwanta da Dumebi a daji, ya kara da cewa haramun ne aikata irin wannan abun a garin.

Mijin Dumebi wanda yaji kunyan abunda matarsa ta aikata ya bukaci da ta bar masa gidansa. Yace “ Na kori matar da abun kunyanta kuma na kona kayanta saboda haramtaccen aikin da tayi kuma bazata taba dawowa gidana ba har abada.”

Allah ya kyauta!

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel