Fada da cin hanci da rashawa: Ana kuka a mulkin Buhari

Fada da cin hanci da rashawa: Ana kuka a mulkin Buhari

– Ma’aikatan Gwamnati sun koka da halin da ake ciki a Najeriya

– Ana fama da masifan rashin kudi

– Shugaba Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Fada da cin hanci da rashawa: Ana kuka a mulkin Buhari

Fada da cin hanci da rashawa: Ana kuka a mulkin Buhari

A wani bincike da wata Jarida tayi an gano cewa Ma’aikatan Najeriya sun koka da irin halin da ake ciki na rashin kudi a Najeriya a wannan mulki na shugaban kasa Muhammadu Buhari. Abin dai har ya kai ga manyan motoci hannun Ma’aikata amma babu kudin zuba masu mai.

Ma’aikatan Najeriya dai sun saba cuwa-cuwa watau ha’inci to yanzu ta kai kowa yana dogara ne da dan albashin sa. Hakan dai ta sa Jama’a na ta cire ‘Ya ‘yan su daga manyan Makarantu masu mugun tsada. Ana dai ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hana mutane damar da suke samu a da.

KU KARANTA: Arewa ta shirya rabewa daga Najeriya

A lokacin baya Najeriya ta samu makudan kudi daga bangaren mai, hakan ya sa aka yi ta facaka, sai dai fa yanzu abubuwa sun canza tun zuwan Muhammadu Buhari. Yanzu haka an maida asusun kudin Kasar zuwa biai daya watau TSA wanda wannan ya kawo sauyi kwarai da gaske.

Wadanda suka saba barna da kudi sun shiga cikin wani hali da ba su saba ba, wasu ma dai na da wasu mutanen dabam a karkashin su. Yayin da kudin sata yayi wuya, sai kowa ya zama kaffa-kaffa. Ko ya za a kare da Yaki da rashawar da wannan Gwamnati ta dauko?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel