Cutar dake damun shugaban kasa Muhammadu Buhari

Cutar dake damun shugaban kasa Muhammadu Buhari

Fadar shugaban kasa ta ce rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari wani sirri ne tsakaninsa da likitansa wanda bai kamata wani mutum ya sani ba.

Cutar dake damun shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Muhammadu Buhari bai koma kasar kamar yadda aka tsara ba ne saboda likitansa ya bukaci ya zauna domin sake duba lafiyarsa.

Ya kara da cewa bayan an gudanar da gwaji a kan shugaban kasar sau daya, an sake yin gwaji a kansa kuma sakamakon gwajin na biyu ake jira shi ya sa likitan ya bukaci Shugaba Buhari ya zauna har sai an fitar da sakamakon.

KU KARANTA KUMA: PDP, APC sun kara kan matsayin lafiyar shugaban kasa

Sai dai ya ce yana fatan ba za a dauki dogon lokaci ba kafin a fitar da sakamakon gwajin na biyu.

Da majiyarmu ta BBC ta tambaye shi kan ko wacce rashin lafiya ce ke damun shugaban kasar, kakakin shugaban kasa Shehu ya ce, "Wannan sirri ne tsakanin mara lafiya da likitansa".

Amma ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi wa shugaban kasar addu'a.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne dai shugaban ya tafi hutu birnin Landa inda yace zaiyi hutun kwanaki 10, ya kuma koma bakin aiki a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel