Karen EFCC ya biyo James Ibori da laifuka 170

Karen EFCC ya biyo James Ibori da laifuka 170

- Hukumar EFCC tana laale marhabun ga tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori da laifuka 170 tun lokacin da yake gidan yarin kasar Ingila

- Wata majiyar EFCC ta tabbatar da cewa wasu laifukan na kotu yanzu kuma za’a gurfanar da Ibori na laifin kokarin baiwa Nuhu Ribadu cin hanci

- Kana kuma ana tuhumarsa da laifin karkatar da kudin jihar Delta N40billion

YANZU-YANZU: Karen EFCC ya biyo James Ibori da laifuka 170

YANZU-YANZU: Karen EFCC ya biyo James Ibori da laifuka 170

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tana shirya damke tsohon gwamnan jihar Delta bayan ya kwashe shekaru 6 a kurkukun kasar Ingila.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa kafin a daure Ibori a kasar Ingila, hukumar EFCC ta kai Ibori wata babban kotun Asaba da laifi 170. Wannan laifuka zai bada daman damke Ibori.

KU KARANTA: Dino melaye ya caccaki Buhari

Daya daga cikin laifukan shine Ibori ya karkatar da kudin gwamnatin jihar Delta N40billion lokacin da yake ofis kuma yayi kokarin baiwa tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu da kudi $15m.

Duk da cewa kotun Asaban tayi watsi da laifuka 170 da akaywa Ibori, hukumar EFCC ta daukaka kara kuma an nada alkalai 3 su zaunan akan al’amarin a ranan 15 ga watan Mayun 2014 wanda ke cewa za’a cigaba da gurfanar da Ibori idan ya gama wa’adinshi a kurkukun Ingila.

Wata majiyar EFCC tace za’a gayyaci Ibori domin amsa tambayoyi.

Majiyar tace: “Ibori nada laifuka 179 akansa. Kuma kotun daukaka kara ta bamu daman cigaba da gurfanar da shi kuma kotun koli bata janye wannan Magana ba.

“Yadda abubuwa suke yanzu, EFCC nada hakkin damke a duk lokacin da ta ga dama. Ana tuhumarsa da laifin karkata kudi N40bn na jihar. Kana kuma yayi kokari baiwa tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, da kudi $15m kudi a hannu.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel