Na shiga ban ɗauka ba, baya fidda ɓarawo

Na shiga ban ɗauka ba, baya fidda ɓarawo

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 33 a gaban kotun garin Ohio dake kasar Amurka bayan an kama shi da laifin kuste gidan wasu mutane inda ya girka ma kansa lafiyayyen girki, har ma ya kara da wanka da ruwan zafi bayan yaci ya koshi.

Na shiga ban ɗauka ba, baya fidda ɓarawo

Jacob Merchant

Yansandan sun bayyana sunan barawon mai suna Jacob Merchant, inda suka ce bashi da matsuguni, don haka gararamba kawai yake yi akan titi, tare da yin kutse gidajen mutane, sai dai baya sata, illa kawai yaci girki ya koshi, kuma yayi wanka, daga bisani sai ya fice.

KU KARANTA: Dan ba ƙara ba: an casa wani barawo ciki da bai

Sai dai a wannan karon, wata mata data kama shi yana wanka a bayinta ta kai kararsa ga hukumar yansanda, kuma ta shaida musu da alamu yayi girki, don taga ya kacalcala mata dakin girki.

Yansanda suna tuhumar sa da laifin yin kutse gidan da ba naka ba, kuma zai gurfana gaban kuliyan nan bada dadewa ba. Sai dai wannan lamari ya sake nuna halin da marasa galihu suke ciki a garin Ohio.

Kalli wannan bidiyon dake nuna yadda ake kama masu kutse a na’urar daukan hoto:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel