Mara imani ne zai yi fatan mutuwan Buhari – Kakakin APC

Mara imani ne zai yi fatan mutuwan Buhari – Kakakin APC

- Kakakin jam’iyya mai ci All Progressives Congress (APC), Bolaji Abdullahi, yace rashin imani ne mutum yayi fatan mutuwan Buhari

- Yayinda yake bayanin cewa ranaku duhu da wahala yak are a Najeriya, ya kara da cewa ba gwamnatin Buhari ne jawo matsin tattalin arziki ba

Mara imani ne zai yi fatan mutuwan Buhari – Kakakin APC

Mara imani ne zai yi fatan mutuwan Buhari – Kakakin APC

Tsohon ministan wasa da matasa kuma kakakin jam’ iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, yace rashin imani ne mutum ya dinga fatan shugaba Buhari ya mutu.

Abdullahi wanda ya bada amsa akan tambaya cewa ana ganin APC a matsayin tsinuwa da wahala a Najeriya , yace matsalolin Najeriya ba yau suka faraba.

KU KARANTA: Labarun da suka faru karshen mako

Amma, yana kyautatta zaton cewa abubuwa zasu farfado Najeriya.

" Ina ganin mutane sun ji mamaki ne, Na fahimci cew mutane na cikin damuwa kuma na san azzalumai na jaddada maganan saboda tayar kura a kasa. Ko lokacin da gwamnatin tace shugaba Buhari zai je jinya ne musamman a wannan shekaru na shi, ana yada jita-jita.

" Mu shugabannin ya kamata mu dinga kyakkyawan zato. A matsayinmu nay an kasa, bai kamata mu dinga tayar da zaune tsaye kan irin wannan abu ba. Bai kamata a yi siyasa kan jita-jitan mutuwan Buhari ba saboda rashin imani ne kayi fatan wani ya mutu.

" Bai kamata mu rasa imaninmu komin wuya. Duk wanda ke farin cikin rashin lafiyan wani bai da imani. Wannan ba maganan gwamnati ko jam’iyya ba ne.”

Zaku tuna cewa shugaba Muhammadu Buhari yace ba zai samu daman dawowa ba yau litinin, 6 ga watan Febrairu,2017 kamar yadda yayi alkawari lokacin da ya tafi Landan.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai

An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai

An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai
NAIJ.com
Mailfire view pixel