PDP, APC sun kara kan matsayin lafiyar shugaban kasa

PDP, APC sun kara kan matsayin lafiyar shugaban kasa

Babban jam’iyyar adawan Najeriya wato jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fada ma yan Najeriya gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki.

PDP, APC sun kara kan matsayin lafiyar shugaban kasa

Jam’iyyar PDP ta yi wannan kiran ne bayan shugaban kasa Buhari ya kara tsawon hutunsa har zuwa lokacin da ba’a sani ba da kuma rashin dawowarsa Najeriya daga birnin Landan.

Jam’iyyar ta PDP tace ba daidai bane shugaban kasa ya aika wasika ga majalisar dokoki, inda ya tsawaita hutunsa ba tare da ya fada wa yan Najeriya ranar dawowarsa ba.

KU KARANTA KUMA: Tsawaita hutun Buhari ya jawo cece-kuce

PDP’s spokesperson Dayo Adeyeye who spoke with Punch newspaper said it was wrong for the President and his handlers to be trivializing the health of the President.

Kakakin PDP Dayo Adeyeye wanda yayi magana tare da jaridar Punch yace ba daidai bane ga shugaban kasa da masu horonsa su dunga daukar lafiyar shugaban kasa da rashin muhimmaci.

“Shugaban kasa ya san cewa shi bad an kasa mai zaman kansa bane.

“Ya kamata ya san cewa yan Najeriya ne ke biyan kudin rashin lafiyarsa kuma don haka, ya fada masu gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki.

“Ya daina daukan yan Najeriya da rashin muhimmanci kuma ya san da cewa abunda za’a iya samu a kasashe masu wayewa. Najeriya ba kurmin daji bane.

“Ta yaya shugabna kasa zaiyi magana game da Karin hutu amma yaki ambatan lokacin da zai dawo?

“Gwaje-gwajen lafiya na da ranakun da za’a karbi sakamako. Ba zai yiwu a fara a kare da tare da rana ba,” cewar sa.

Gurin maida martani ga kiran PDP, babban sakataren labarai na jam’iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya tambayi PDP inda ya bayyana cewa “Shin PDP su san fiye da abunda aka fada mana ne? abunda muka sani shine abunda aka fada mana.”

“Wannan shine shugaban kasar. Zabe ya kare; shine shugaban kasarmu, ya kasance shugaban kasar Najeriya ba wai na jam’iyyar APC ko PDP ba. Idan shugaban kasar ya fada masa cewa yana bukatar kara tsayawa a can don yin wasu abubuwan da suka shafi lafiya, yana gaba damu, a matsayin yan kasa masu biyayya, ayi masa addu’a sannan a daina amfani da daman gurin kai hari.

“Shin PDP su san fiye da abunda aka fada mana ne? abunda muka sani shine abunda aka fada mana.

“Mun yarda cewa shugaban kasa yayi dukkan ayyukan da ya ta’allaka a kansa. Dukkanmu shedu ne a kan abubuwan da suka faru a baya inda shugaban kasa zaiyi tafiya kuma yaki mika ma majalisar dokoki takardun da suka dace da zai sa mataimakin shugaban kasa a lokacin zama mukaddashin shugaban kasa.

“Amma wannan ya kasance shugaban kasar da a koda yaushe zaiyi tafiya, yake ba mataimakinsa daman yin aiki a matsayin shugaban kasa a bayan sa.

KU KARANTA KUMA: Kotun Amurka ta dakatar da dokar Trump na hana musulmai shiga kasar

“Ban san dalilin da yasa mutane suka fara canja kalar idanunsu ba kamar dama can muna sa ran abu mara dadi ya faru da kasar nan ba.

“Yan PDP su daina halin da zai say an Najeriya su fara tunanin cewa lallai suna yada jita-jitan cewa shugaban kasar ya mutu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel