Makiyaya na wa matan mu fyade – Inji kungiyar Igbo

Makiyaya na wa matan mu fyade – Inji kungiyar Igbo

Wani jigon kabila Igbo a Jihar Ebonyi, shugaba Abia Onyike, ya zargi Fulani makiyaya da cewa a kwanan nan sun zama kungiyar ‘yan ta’adda masu aiwatar da kisan gillar ga kabila Igbo a Najeriya.

Makiyaya

Makiyaya

‘Yan kungiyar zamantakewa da siyasa ta kabila Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta bayyana cewa, sananne Fulani makiyaya sun ci gaba da kashe-kashe, yin fyde da matansu da kuma hallaka kayan gonakin su.

Shugaban kungiyar shugaba Nnia Nwodo ya bayyana wannan labari a lokacin da yake magana da jaridar Vanguard.

A baya akwai zaman lafiya da kauna tsakanin magabata Fulani makiyaya da kuma mutanen yanki, wandannan makiyaya na kiwo shanunsu tare da dogon, amma a halin yanzu an yi gurbinsu da yawo da bindigar zamanin AK-47 tare da hallaka mutane da gonakin mu.

KU KARANTA KUMA: Mutane 8 mafi kaunar shugaba Buhari

Ba bu daya daga cikinsu da haka kama domin mallaki bindigogi ba bisa doka ba, Ko kuma wadanda aka kama a garin Nimbo da rikicin kashe-kashen al’umma, ba hukunta su ba sabili da ‘yan arewa ne suka fi yawa a jami'an tsaro.

Har ila yau a cikin jihar Abia, Sakataren gwamnatin jihar Abiya, Dr. Eme Okoro, ya koka a kan rikicin Fulani makiyayan ga mutanen yankin, ya kuma bukaci shugaban kasar Buhari ya kira su zuwa ga oda.

Babu wata bangaren al’umma Bende da Fulani makiyaya ba su kai farmaka ba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel