Tsawaita hutun Buhari ya jawo cece-kuce

Tsawaita hutun Buhari ya jawo cece-kuce

- Dr Junaid Mohammed ya bukaci yan Najeriya da su dauki makomar su a hannayensu

- Yayi ikirarin cewa akwai wani makirci a gwamnati kamar lokacin gwamnatin Yar’Adua

- Gwamna Fayose ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Dr Junaid Mohammed ya bukaci yan Najeriya da su kasance masu kula a wasikar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga majalisar dokoki inda ya nemi Karin hutu.

Ansa ran shugaban kasa zai dawo kasar a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu amma ya rubuta wasika ga majalisar cewa bazai samu dawowa ba kamar yadda aka tsara sakamakon wasu gwaje-gwaje da yake jira.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mohammed yayi ikirari cewa wani makirci ya fara aiki don kwace gwamnatin kamar yadda ya faru a lokacin gwamnatin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, matarsa da wasu yan siyasa suka saka yan Najeriya cikin duhu.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin dan Bala Mohammed kan naira 100m

Yace: “Ci gaba game da lafiyar shugaban kasa daga dukkan alamu abune mai munin gaske kuma abun takaici ne Najeriya ta kara risker kanta cikin wani tashin hankali. Haka kuma abun takaici ne Buhari da masu kula dashi suna kokarin haddasa wani rikici maimakon su fada way an Najeriya gaskiya. Wannan ya zo shige da na Yar’Adua lokacin da wasu makirai tare da taimakon matarsa suka rike kasar ga fansa da kuma yaudaran yan Najeriya”.

Ina ganin ya kamata Yan Najeriya su tashi tsaye kan wannan idan majalisar dattawa bazasu iya tsige shugaban kasar wanda a yanzu ya kasa aikin sa a matsayin shugaban kasar Najeriya.

“Akwai alamun cewa masu makarkashiya basa son kawo karshen wannan kuma shiyasa suke wasa da hankulanmu. Wadannan na daga cikin wasu abubuwan da muka hango kuma muna ta ihun cewa ya kamata a fada ma yan Najeriya gaskiya game da lafiyar shugaban kasa. Ina addu’a kan Allah ya taimaki yan Najeriya amma ya zama dole yan Najeriya su dauki makomarsu a hannayensu.”

A nasa martanin, Gwamna Ayo Fayose wanda ya kasance babban dan adawan gwamnatin Buhari ya bukaci yan Najeriya da suyi ma shugaban kasa addu’a.

Yace: “Me ya rage zance da ya wuce na bukaci yan Najeriya da suyi masa addu’a?”

Mista Kayode Ajulo ya kasance mai kare hakkin yan adam ya bayyana cewa babu wani doka da ya kayyade lokacin da shugaban kasa zaiyi a hutu amma cewa likitan shugaban kasa ne ya kamata ya hadu da majalisar dokoki ba wai shi Buhari ya aiko da wasika ba.

Yace: “Idan aka zo kan al’amarin hutun shugaban kasa, babu wani doka da ya kayyade iya lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu. Amma idan yazo da rudani, abunda kawai yake a bayyane shine shugaban kasa ma jami’in gwamnati ne kuma dokar dake kewaye da ko wani jami’in gwamnati shi ke kewaye dashi.

“Najriya na muke ciki a yau, iya adadin kwankin da ko wani jami’in gwamnati zai iya tafiya hutu wata daya ne sai dai idan akwai bashin hutu da baiyi ba. Don haka idan ya tafi hutun kwanaki goma na yarda cewa yana da sauran ranaku da ya saura masa.

“Sannan abu na biyu, wannan Karin hutun karara ya nuna cewa shugaban kasar mu baida lafiya. Ya kamata ace muyi duba ga sashin kundin tsarin mulki da yayi magana game da gazawar shugaban kasa domin sanin idan shugaban kasa na bukatar likita na musamman da zai kula da lafiyarsa.

“Ina ganin a maimakon wannan wasikar, likitan nasa ne ya kamata ya hadu da majalisar dokoki don tabbatar masu da halin da lafiyar shugabna kasa ke ciki. Wannan shine abunda kundin tsari mulki ya yarda da saboda idan aka zo kan al’amarin lafiya abune mai muhimmanci kuma kundin tsarin mulki yayi tanadi a kan haka.

KU KARANTA KUMA: Kotun Amurka ta dakatar da dokar Trump na hana musulmai shiga kasar

“Yanzu likitan da bamu sani ba. Yana wata uwa duniya. Tambaya anan shine tayaya mutumin da baida lafiya ya rubuta wasika? Ba sai an yaudare mu ba. Muna yiwa shugaban kasa fatan samun lafiya, muna yi mai fatan dawowa kasar nan, muna son sa amma nayi magana ne a matsayin lauya. Akwai bukatar likitan shugaban kasar ya hadu da yan majalisar dokoki."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel