Abubuwan 5 da zai faru idan Buhari bai dawo ranar Litini ba

Abubuwan 5 da zai faru idan Buhari bai dawo ranar Litini ba

‘Yan Nijeriya sun masu da dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga hutu na ranar 10 a kasar Britaniya.

Abubuwan 5

‘Yan Nijeriya na cikin wata rudanin game da lafiya shugaba Muhammadu Buhari da kuma jita-jitar mutuwarsa. Karin Tsawon rana daga hutunsa ya jefa al'umma cikin wata rashin tabbas.

Duk da haka, akwai abubuwa 5 wanda lalle ne ta faru idan shugaban kasa ya gaza dawowa a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

1. Osinbajo zai ci gaba

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai ci gaba da jagorantar harkokin kasa kamar yadda ya saba bayan tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Za a tuna cewa a cikin lokacin da shugaba Buhari ya fara hutu, Osinbajo ya gudanar da wata taron da mambobin sawainiya ta karkashin shugaban kasa a kan farashin abinci a Najeriya.

Shugaban mai rikon kwariya ya jaddada cewa gwamnati na matukar damuwa da tashe-tashen farashin abinci a kasuwa.

2. Matasa 15,000 za su koma da bacin rai

Matasa 15,000 wadan da a ke zato za su tarbi Shugaban Muhammadu Buhari a lokacin da zai dawo daga hutu na kwana 10 a kasar Britaniya za zu koma gida da bcin rai.

Duk da haka, za su ci gaba da yin addu'a da kasancewa shugaban kasa ya zamu isashen lafiya.

3. Za a kara karfafa jita-jita

Tun dama akwai jita-jitar mutuwar shugaba Buhari, wadannan mutane masu jita-jitan za su samu wata dammar sake yayada wannan labara.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ba zai dawo gobe ba saboda wadannan dalilai

4. Fadar Shugaban kasa za ta kare tsawon hutun

Fadar shugaban kasa za ta zamu kan ta cikin wata matsayin kare dalilin Karin tsahon hutun shugaban kasa. Tuni fadar shugaban kasa ta bayar da wata sanarwa game da lafiyar shugaban kasa cewa shugaba Buhari na cikin koshin lafiya.

5. Za a matsa lambar tsigewa da murabus

Akika mutane za su matsa wa shugaban kasa lamban tsigewa da kuma kira ya yi murabus. Tuni ake zargin fada shugaban kasa rashin sanar da ‘yan Najeriya matsayin shugaban kasa.

Wasu za su kira shugaban kasa ya yi murabus wasu kuma za su yi kira da a tsige shi.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel