Dan ba ƙara ba: an casa wani barawo ciki da bai

Dan ba ƙara ba: an casa wani barawo ciki da bai

Jama’an garin Soweto na kasar Afirka ta kudu sun shahara wajen ladabtar da duk wanda suka kama yana kokarin satar kayayyakin su musamman wanda suka sha wahala wajen samunsa.

Dan ba ƙara ba: an casa wani barawo ciki da bai

Motar barawon yayin da aka juya ta

Da haka ne suka casa wani mutumi da suke tuhuma da sata yayin dayayi kokarin satan wani katin cire kudi wato ATM a wani katafaren shagon siyayya mai suna Protea Gardens Mall.

KU KARANTA: Wata ýar koyan aiki tayi basaja ta sace ýar uwarɗakinta

“Barawon na cikin motarsa kirar VW Polo yayin dayake kan hanyarsa ta zuwa katafaren shagon, isan sa shagon ke da wuya sai yayi kokarin satar katin cire kudi, wanda hakan ya ja masa cin dukan tsiya a hannun mutanen dake wajen bayan sun fusata,” inji Kaakakin yansandan Protea Glen.

Dayake akwai na’urar daukan hotuna a shagon, an dauki hoto da bidiyon dukan da mutumin ya sha, inda a ciki aka ga mutanen sun daga motar sa sama suka juya ta tare da farfasa gilasan motar kafin daga bisani suka janyo barawon waje daga cikin motar, kuma suka cigaba da casa shi.

Kaakakin yansanda yace “jama’a sun cigaba da suburbudan barawon har sai da yansanda suka iso inda lamarin ya faru suka tseratar da shi, inda suka garzaya da shi asibiti.”

Sai dai bayan kwana daya ne aka sallami barawon daga asibiti, kuma yansanda sun cigaba da gudanar da bincike kan lamarin. ga bidiyon yadda lamarin ya kasance a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel