Gwamna Okowa yayi alkawarin dagewa da yi ma jiharsa addu’a

Gwamna Okowa yayi alkawarin dagewa da yi ma jiharsa addu’a

Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Kowa ya bayyana cewar ya yanke shawarar tsuke bakinsa tare da kara kaimi wajen yin addu’ar samun cigaba a jihar sa da kasa gaba daya, duka da irin adawar da abokan hamayya zasu dinga nuna masa.

Gwamna Okowa yayi alkawarin dagewa da yi ma jiharsa addu’a

Gwamna Okowa

Okowa ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 5 ga watan Feburairu, yayin dayake jawabi a taron cocin Peace Foundation Bible Ministry karo na 20 daya gudana a garin Asaba.

KU KARANTA: Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram guda 5

Gwamnan ya nuna damuwarsa da karuwar ayyukan masu garkuwa da mutane, masu fasa bututun mai da sauran miyagun ayyuka daban daban a jihar, wannan ya sanya gwamnan shaida ma mahalarta taron cewar ba zai bari yan adawa su dame shi ba, don haka ne zai dage da yi ma jihar addu’a.

Gwamnan yayi kira ga mabiya addinin kirista dasu rage kwadayin duniya, a maimakon haka su dage da yi ma kasa addu’a tare da kokarin dawo da martaban kasar, inda yace yawancin malaman addininan kirista basa nuna ma mabiyansu amfanin kusantan ubangiji, wanda hakan ke sanya mutane shiga aikata miyagun laifuka.

Gwamna Okowa yace addu’a ne kadai mafita daga wannan halin karayar tattalin arziki da kasar ta samu kanta a ciki.

Shima babban limamin cocin, Bishop Prayer Okoh ya bukaci mabiya addinin kirist dasu hada kawunansu, kuma su dage wajen kusantan ubangiji mahillicinsu, inda ya caccaki wasu limaman addinin na kirista daya ce sun gaza a aikin tarbiyyantar da mabiyansu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel