A fagen siyasa na kai matsayin Farfesa-Inji Fayose

A fagen siyasa na kai matsayin Farfesa-Inji Fayose

– Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti yace in dai aka zo fannin siyasa to ya kai Farfesa

– Ayo Fayose yace an dade ana gwabzawa da shi

– Gwamna Fayose yace shi kada ne ba ya jin tsoron shugaba Buhari

A filin siyasa na kai matsayin Farfesa-Inji Fayose

A filin siyasa na kai matsayin Farfesa-Inji Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose yace idan aka shigo fannin siyasa ya kai matasayin Farfesa. Gwamna Ayo Fayose yace shi hukuma ce mai zaman kan ta idan dai ana maganar siyasa a cikin Kasar nan.

Ayo Fayose yace an dade ana bugawa da shi tun ba yau ba. Gwamna Fayose yace kowa dai ya buga ya bar sa. Gwamnan yace shi kadai ne ba ya jin tsoron Buhari don kuwa babu irin sa. Fayose yace yayi Gwamna lokacin Obasanjo, ya kuma yi lokacin shugaba Jonathan sannan lokacin Buhari.

KU KARANTA: EFCC ta daskare asusun Fayose

Fayose ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da Jaridar Punch. Fayose yace ko ‘Yan Jam’iyyar APC sai dai su shafa masa lafiya don kuwa ya kai Farfesa a fagen siyasa. Daga baya ma dai mun samu labarin Gwamnan yace an nuna masa cewa zai mulki Kasar nan.

Kwanan nan Gwamna Fayose ya kira Gwamnatin tarayya ta kara kudin masu bautar Kasar zuwa N50, 000. Gwamnan ya nemi a karawa matasan Kasar albashi don kuwa yanzu N 19, 8000 babu inda za ta.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel