Fasto Mbaka ya soki na-kusa da Buhari

Fasto Mbaka ya soki na-kusa da Buhari

– Wani babban Fasto yayi kaca-kaca da na kusa da Buhari

– Fasto Mbaka yace wadanda ke zagaye da shugaban kasa ba mutanen arziki ba ne

– Mbaka yace wadanda su ke kusa da Buhari aljihun su suke karewa

Fasto Mbaka ya soki na-kusa da Buhari

Fasto Mbaka ya soki na-kusa da Buhari

Babban Faston nan na Cocin Adoration da ke Jihar Enugu yayi kaca-kaca da wadanda ke zagaye da shugaban kasa Buhari, yace sam ba mutanen arziki ba ne kuma aljihun su kurum su ke kokarin karewa.

Fasto Ejike Mbaka yace Buhari na da niyya mai kyau, amma fa wasu na kokarin ganin hakan bai yiwu ba. Fasto Mbaka yace na kusa da shugaban kasa Buhari ba abin da ya dame su da gyara Najeriya su dai kurum kan su suke kokarin gyarawa.

KU KARANTA: Ku daina yi wa Buhari fatan mutuwa-OBJ

Faston yayi wannan jawabi ne a wani gagarumin huduba da yayi a Cocin sa. An dai san Faston da goyon bayan Buhari tun ba yau ba. Fasto Mbaka ya kuma soki masu fatan shugaba Buhari ya mutu, yace masu fadar haka ba su kaunar Najeriya.

Haka tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yayi Allah-wadai da masu kirawa shugaba Buhari mutuwa. Tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi kira ga duk wadanda ba su kaunar shugaban kasar da su tinkari zabe mai zuwa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Babban Mawaki ya fasa zanga-zangar Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel