EFCC ta karbe gidan wani tsohon Gwamna

EFCC ta karbe gidan wani tsohon Gwamna

– Hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamna Isa Yuguda

– Wata Kotu ce ta ba EFCC damar karbe kayan tsohon Gwamna na Bauchi

– Ana binciken Yuguda da laifin satan dukiyar Jama’a

EFCC ta karbe gidan wani tsohon Gwamna

EFCC ta karbe gidan wani tsohon Gwamna

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta karbe wasu kaya na tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda. Wannan ya biyo bayan wani babban Kotun tarayya da ke Abuja ta ba Hukumar damar hakan.

Yanzu haka dai Hukumar ta EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamna Yuguda da ke Unguwar GRA na Bauchi. Wani Jami’in Hukumar EFCC yace za a rike gidan ne na wani dan lokaci kafin a kammala bincike.

KU KARANTA: Kotu ta bada belin Dan Minista

Ana zargin tsohon Gwamnan da laifin satar kudin Jama’a da wuce gona da iri lokacin yana kan kujera. Alkali J. Tsohon na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba Hukumar EFCC damar karbe kayan tsohon Gwamnan a wancan makon.

Har wa yau Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tana zargin tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da karkatar da wasu Naira Biliyan 2.8. Yanzu haka dai ana ta shari’a a babban Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Buhari da Mutanen Bauchi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel