Duk wanda bai son Buhari ya jira 2019

Duk wanda bai son Buhari ya jira 2019

– Tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ya soki masu yi wa Buhari mugun fata

– Obasanjo yace duk wanda bai son Buhari ya tinkari zabe mai zuwa

– Cif Obasanjo yace haka aka yi masa lokacin yana kan kujera

Duk wanda bai son Buhari ya jira 2019

Duk wanda bai son Buhari ya jira 2019

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yayi Allah-wadai da masu kirawa shugaba Buhari faran mutuwa. Tsohon shugaban kasa yayi kira ga duk wadanda ba su kaunar shugaban kasar da su tinkari zabe mai zuwa.

Obasanjo yayi wannan magana ne ta bakin mai magana da yawun sa a wancan makon a Garin Abeokuta. Olusegun Obasanjo yace masu fatar Shugaba Buhari ya mutu ba su da imani da kuma tausayi ko na sisin kwabo.

KU KARANTA: An shirya tarbar Shugaba Buhari

Obasanjo yace duk wanda bai son Buhari ya jira zabe mai zuwa a shekarar 2019 sai ya zabi wannan dabam. Obasanjo ya nemi a taya shugaban kasar da addu’a yana mai cewa haka aka yi da shi lokacin yana mulki.

Yanzu haka dai shugaba Buhari ya fasa dawowa daga hutun da ya tafi, ya kuma bayyana dalilan sa na yin hakan. Ana sane cewa Sheikh Jingir Malamin Kungiyar nan ta Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ya soki masu kirawa shugaba Buhari mutuwa a wancan makon.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel