Yadda direban Audu Maikori ya damfareshi da karyar kashe-kashen kudancin Kaduna

Yadda direban Audu Maikori ya damfareshi da karyar kashe-kashen kudancin Kaduna

- Direban Audu mai Kori wani atatajri ya yi masa karya game da kisan da makiyaya su ka yi a kwalejin ilimi ta Kaduna

- Mai tukin motar na sa ya yi karya ga mai gidansa cewa makiyayan sun kashe masa dan uwa wanda ya sa mai gidan nasa ya yi kira gwamnan jihar don tsayar da kashe-kashen sakamakon da kimara ta zube a idonsa da ya gano karya ne

Yadda direban Audu Maikori ya damfareshi karyar kashe-kashen kudancin Kaduna

Yadda direban Audu Maikori ya damfareshi karyar kashe-kashen kudancin Kaduna

Direban Audu Maikori wani attajiri mazaunin Legas ya sa shi cikin rudani bisa zargin kashe dalibai a kwalejin Ilimi ta Kaduna da a ke zargin Fulani makiyaya sun yi ranar Juma'a 27 ga watan Janairu a 2017.

Wannan ya sa Maikori da ya watsa lamarin kisan a dandalin sada zumunta na Tuwita, yanzu kuma ya ke neman afuwa ga gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai bisa labarin kanzon kurege na cewa Makiyaya sun kashe daliban kwalejin Ilimin.

Attajirin ya bayyana cewa: "Direba na Simon Joseph ya je kauyensu halartar taron binne kaninsa kuma a dawowarsa ranar Litinin 30 ga Janairu 2017, na tambaye shi hotunan taron da katin shaida zuwansa sannan da hotunan makarar don na mikawa hukukomi sai ya ce yana da matsala da wayarsa shi ya sa ba ya ajiye hotuna a wayar.

"Ya ce min 'yar uwarsa ta na da hotunan a wayarta sai na bashi kudi ya je Ikeja ya karbo hotunan a wajen 'yar uwar tasa, ko na nuna don wanke kaina.

"Bai dawo ba har yamma kuma da ya dawo sai gashi ba hotunan. A nan ne na fara saka alamar tambaya. Sai na kara tambayarsa game da sahihancin labarin da ya rantse da Bible cewa dan uwansa ya rasa ransa har ma ya fara zubar da hawaye."

Maikori ya ci gaba da cewa, Cikin kokwanton lamarin direban nasa, ya dauke shi da danginsa zuwa ofishin 'yan sanda na Lekki a ranar 2 ga Fabrairu inda daga baya ya amince ya fadawa mai gidan nasa don ra'ayinsa ko ya dan samu kudi a wajensa.

"Yayin da mu ka shiga ofishin, sai ya kara cewa labarin nasa gaskiya ne har sai da 'yan sandan su ka yi masa bayani cewa za a tsare shi. Sannan ya amince cewa, kokari kawai ya ke na karbar kudi a wajena; tun da ya san ina taimakawa a kan sha'anin rikicin na kudancin Kaduna shi ne ya so ya yi amfani da wannan dama ya samu kudi a wajena da nufin bikin binne gawa."

Da ya ke neman afuwa ga hukukomin da abin ya shafa, ya rubuta cewa:

"A wautata na dauka ba wani da ya ke cikin hankalinsa da zai yi karya game da mutuwar wani musamman dan uwa. A sakamakon haka, ina mai matukar neman gafarar hukumar kwalejin Ilimi Gidan Waya da gwamnan jihar Kaduna da gwamnatin jihar Kaduna da kuma jama'ar kudancin Kaduna da al'ummar Fulani bisa labarin karya da direbana ya yi wanda na yayata ina tunanin gaskiya ne."

"Ina wannan jawabi ne da zuciya daya duk da na gano cewa ta hanyar amincewa da abinda ya faru, mutane za su fara kokwanton gaskiyar duk abinda zan fad a nan gaba...wannan shi ne taron aradu da ka da zan yi, amma na garace na fadi gaskiya akan lamarin."

Duk da neman afuwar, Maikori ya ce ba yana nufin zai watsi da mutanen sa ne da na kudancin Kaduna da kuma tashin hankalin da su ke ciki. Ya ce neman afuwar tasa ya takaita ne da abinda aka yi zargin ya faru kwalejin Ilimi.

ku biyo mu a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com ko kuma Tuwita a http://twitter.com.naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis
NAIJ.com
Mailfire view pixel