El-Rufai da Buratai sun shimfida harsashin samar da zaman lafiya mai dorewa

El-Rufai da Buratai sun shimfida harsashin samar da zaman lafiya mai dorewa

- Nasiru El-Rufai ya ce kafa bataliyoyin guda 2 a kudancin na Kaduna, ya cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zaben shekarar 2015 na tsare lafiya da dukiyoyi

- Gwamman ya jaddada cewa za a gurfanar da wadanda ke rura wutar rikicin ko da kuwa dansa ne

El-Rufai da Buratai sun shimfida harsashin samar da zaman lafiya mai dorewa

El-Rufai da Buratai sun shimfida harsashin samar da zaman lafiya mai dorewa

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai tare da babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai sun kafa harsashin gina bataliyar sojoji a ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu don tabbatar da tsaro a kudancin jihar Kaduna.

Da ya ke bayanin sabuwar bataliyar da ta ke a Kafanchan, shelikwatar karamar hukumar Jama'a a gaban gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da masu rike da sarautun gargajiya da kuma manya-manyan jami'an soji, Buratai ya ce ,mutanensa za su kwakulo duk wata maboya a cikin daji da tsaunuka don zaluko 'yan ta'addan da ke addabar yankin.

Buratai ya sanar cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa bataliyar sojoji guda 2 a kudancin Kaduna don dawo da zaman lafiya ba tare da sun dauki bangare ba kamar yadda ya ce.

Babban hafsan sojin kasan ya yabawa goyon bayan da gwamna El-Rufai ke bawa jami'an tsaro da ke kokarin dakile rikicin a kudancin Kaduna.

Buratai wanda tun da fari sai da ya kai ziyarar ban girma ga basaraken gargajiya na Kagoro, Ufuwai Bonet da sarkin Jama'a, Alhaji Muhammad Isah, a fadojinsu, ya ce ya zo kudancin Kaduna ne don ya hadu da jami'an sa da aka turo yankin don samar da zaman lafiya.

A cewarsa:

"Na zo nan ne don ziyarar aiki ga sojojin da aka turo kudancin Kaduna. Ya na daga al'amurana na yau da gobe, ziyarar sojojinmu. Bangare ne na hakkin da tsarin mulki ya kallafa mana, mu kare tsayuwar kasarmu sannan mu samar da tsaro a kasa.

"Mu na godiya ga shugaba Muhammadu Buhari da ya amince da samar da cibiyoyin soja guda 2 a kudancin Kaduna. Muna yabawa sarakunan gargajiya bisa goyon bayan da su ke bawa sojojinmu. Muna fata yanayin da a ke ciki a wannan bangare na Kaduna ya zo karshe."

Muna kira ga kowa da kowa da a zauna lafiya da juna. A tarihi, ba za ka iya raba masu kiwo da manoma ba kuma akwai bukatar su zauna lafiya. Zube sojojinmu na nufin zaman lafiya ya dawo."

A nasa bangaren, gwamna Nasiru El-Rufai ya ce kafa bataliyoyin guda 2 a kudancin na Kaduna, ya cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zaben shekarar 2015 na tsare lafiya da dukiyoyi ya na mai jaddada cewa za a gurfanar da wadanda ke rura wutar rikicin ko da kuwa dansa ne.

El-Rufai wanda ya ke cike da fatan kawo karshen hare-hare da kashe-kashe a yankin, ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kudirinsa na kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa sama da shekaru 35.

Majalisar matasan kiristocin Arewa ta yabawa babban hafsan sojin kasa Laftanal janar Tukur Buratai bisa kafa harsashin gina barikin soja a Kafanchan karamar hukumar Jama'a ta jihar Kaduna a wani cigaba da zai taimaka matuka wajen magance ta'addancin makasan da su ka mayar da al'ummu da dama wajen zaman makoki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel