Hukumar EFCC ta sake daskare asusun bankin Fayose

Hukumar EFCC ta sake daskare asusun bankin Fayose

- Gwamna jihar Ekiti, Mr Ayodele Fayose, yace hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, ya daskarar masa da asusun bankinsa ta Zenith Bank

- Fayose yace lokacin da yaje bankin, ma’aikatan sunce sun hana shi ne saboda wata wasika da hukumar ta bata

- Jastis Taiwo Taiwo a watan Disamba ya bada umurnin cewa EFCC saki asusun Fayose

Hukumar EFCC ta sake daskare asusun bankin Fayose

Hukumar EFCC ta sake daskare asusun bankin Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Mr Ayodele Fayose, ya tuhumci hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, ya daskarar masa da asusun bankinsa guda 2 na Zenith Bank, shiyar Ado-Ekiti.

Gwamnan ya sha alwashin kalubalantar abinda wannan hukumar yaki da rashawa ke masa.

KU KARANTA: Jonathan ya gargadi Buhari

Jaridar DailyTrust ta bada rahoton cewa gwamna Fayose, wanda yayi bayani a ranan Asabar, 4 ga watan Febrairu a Ado-Ekiti a wata hira da yan jarida, inda yace ya tafi bankin a ranan Juma’ a3 ga watan Febrairu a Ado-Ekiti amma aka hana shi cire kudinsa duk da cewa akwai hukuncin babban kotu cewa a sake masa asusunsa da aka daskarar.

A watan Disamban 2016, Jastis Taiwo Taiwo ya yanke hukuncin cewa hukumar EFCC ta saki asusun Fayose, amma hukumar yaki da rashawar da kanta ta bukaci kotun ta dakatar da hukuncin amma kotun tayi watsi da ita.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel