Janar Babangida ya dawo bayan jinya a kasar Switzerland

Janar Babangida ya dawo bayan jinya a kasar Switzerland

Tsohon shugban kasan Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya dawo Najeriya bayan yayi kwanaki 7 yana jinya a kasar Switzerland.

Janar Babangida ya dawo bayan jinya a kasar Switzerland

Janar Babangida ya dawo bayan jinya a kasar Switzerland

Ya sauka a babban filin jirgin sama garin Minna a yammacin asabar misalin karfe 6:45 na yamma.

Yayinda yake sauka daga jirgi, Janar Babangida ya nuna godiyarsa bisa ga addu’oin da mutane da dama sukayi masa yayinda ya tafi jinya.

KU KARANTA:

Yace: “ Ina jin dadi yanzu kuma na samu sauki. Wajibi ne in mika godiyata gay an Najeriya bisa ga addu’o’insu da kuma kularsu akan lafiya ta. Ina amfani da wannan dama domin kira gay an Najeriya su cigaba da yima shugabanninsu addu’a da kuma kasa gabaki daya saboda cigaba.

“Mu kasance tsintsiya madaukrinki daya wajen samun cigaba ta hanyar tunani mai kyau akan shugabanninmu da kuma kushesu ta kafa mai kayu.”

Akan abinda kasan ke ciki, IBB yace matsin tattalin arzikin da ake ciki ba Najeriya kadai bane. Yace : “ Ina sane da cewa wasu kasashe na fuskantar kalubale na siyasa, rayuwa da tattalin arziki. Ina kyautatta zaton cewa wanna gwamnati na aiki tukuru domin magance wasu abubuwan.”

“Wajibi ne mu bada goyon baya ga dukkan bangarorin gwamnati domin farfado da tattalin arzikin kasa.”

Janar Babangida ya tafi jinya ne a ranan 18 ga watan Disamba, 2016.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel