Shugaba Buhari na shirin dawowa

Shugaba Buhari na shirin dawowa

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin dawowa Najeriya

– Buhari ya tafi hutu Kasar Birtaniya tun watan jiya

– Zuwa gobe Shugaban kasa Buhari zai shiga Ofis

Shugaba Buhari na shirin dawowa

Shugaba Buhari na shirin dawowa

Idan ba a manta ba Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Najeriya ne a Ranar 19 ga Watan Junairu inda ya tafi hutu Kasar Birtaniya. To da alamu dai jirgin Shugaban kasar ya fara shirin tashi don kuwa lokacin dawowan sa gida yayi.

Shugaba Buhari ya nemi Majalisa ta san da tafiyar sa zuwa hutun inda ya kuma nemi Mataimakin sa Yemi Osinbajo ya zama Mukaddashin sa har sai ya dawo. Zuwa gobe dai ake sa ran cewa Shugaba Buhari zai shiga Ofis.

KU KARANTA: Ku taya Buhari da addu'a Inji Shugaban APGA

Shugaba Buhari na shirin dawowa

Shugaba Buhari na shirin dawowa

A lokacin da ba ya na nan an ta yada jita-jita iri-iri cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu a can. Har sai da ta kai an fito da hotunan sa inda yake shakatawa kana wasu su ka yarda yana raye. Kungiyar nan ta Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta soki masu kirawa shugaba Buhari mutuwa. Kungiyar ta ce kowa idan lokaci yayi zai mutu.

Wata Kungiya mai suna NYCN ta matasan Najeriya dai za ta shirya taron gangami na mutane 1500 domin murnar dawowan Shugaba Buhari.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel