Ra’ayi: Shin za a raba Najeriya kuwa?

Ra’ayi: Shin za a raba Najeriya kuwa?

– Ya ci ayi tambaya wai shin me mutanen Biyafara suke nema ne?

– Shugabancin Kasar nan su ke so ko kuma warewa suke so su yi?

– Imyamurai dai sun samu komai ban da Mulkin Kasar nan

Ra’ayi: Shin za a raba Najeriya kuwa?

Ra’ayi: Shin za a raba Najeriya kuwa?

Ya ci ace ayi tambaya wai me mutanen Kasar Biyafara suke nema ne? Shin Shugabancin Kasar nan suke bukata ko kuwa Kasar kan su suke nema. Wani Marubuci Clem Aguiyi yayi rubutu a game da wannan Ma’udu’i.

Inyamurai a Najeriya dai Mutane ne masu ilmi da basira ga hazaka musamman wajen kasuwanci, sun tara komai sai dai kash, sun kasa samun Mulkin Kasar nan watau Shugabancin Najeriya. Watakila hakan ta sa suke gani an ware su, har suke neman Kasar kan su ba tare da dandara da abin da ya faru baya ba.

KU KARANTA: Mu godewa Allah muna da Buhari Inji wani Gwamna

Musamman zuwan Mulkin Buhari wasu Mutanen Yankin na Biyafara sun kara dagewa wajen fafutukar neman a tsaga su daga Najeriya. Har ta kai Hukuma ta damke wanda har yanzu yana hannu Nnamdi Kanu.

Yanzu haka dai Manyan ‘Yan Siyasan Inyamurai irin su Orji Uzor Kalu, Ken Nnamani, Andy Uba dsr sun shiga cikin tafiyar APC kamar yadda Gwamnan Imo Rochas ya taba kira. Jiya ma wata Kungiya tace idan Kanu zai yi kataborar sa, ya daina kiran su. Yanzu sai ka tambaya mai Inyamurai su ke so, Kasar kan su ko Shugabanci?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel