Jonathan ya roki Trump ya taimakawa Najeriya

Jonathan ya roki Trump ya taimakawa Najeriya

– Tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck yayi magana a gaban Majalisar Kasar Amurka

– Jonathan Goodluck ya bayyana irin matsalolin da ake fuskanta a Najeriya

– Jonathan ya nemi Shugaba Trump ya taimaki Kasar Najeriya

Jonathan ya roki Trump ya taimakawa Najeriya

Jonathan ya roki Trump ya taimakawa Najeriya

A farkon wannan Watan Tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Amurka inda aka gayyace sa domin yayi magana game da matsalolin Najeriya musamman rikicin addini da sauran su.

Jonathan ya fara da godewa Sanata Chris H. Smith wanda shine Shugaban Kwamitin harkokin Afrika a Majalisar Kasar Amurka da irin kokarin sa har da zuwa Yankin Neja-Delta na Najeriya domin ganin yadda abubuwan suke tafiya.

KU KARANTA: Wani Babban Fasto ya Musulunta

Jonathan ya gargadi Gwamnati mai-ci da ta guji amfani da karfi wajen shawo kan matsalolin Yankin na Neja-Delta yace hakan zai tada babban fititna. Jonathan Goodluck ya kuma yi magana a kan rikicin Kudancin Kaduna wanda yace idan aka duba Gwamnatin sa duk tayi nazarin yadda za a shawo kan wannan matsaloli.

Kwanan nan dai gwamnatin tarayya tace za ta cigaba da biyan Mutanen Neja-Delta kudin da aka saba su. Sannn kuma a jiya ne Shugaban Hafsun Soji Janar Buratai da Gwamna El-Rufa’i suka gana domin bude Gidan Soji a Yankin na Kudancin Kaduna.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel