Kasar Amurka sun ce ba ruwan su da wata takardar Biyafara

Kasar Amurka sun ce ba ruwan su da wata takardar Biyafara

– Kasashen Amurka da Birtaniya sun ce ba ruwan su da takardun Biyafara

– Amurka da Ingilar dai sun ce bai halatta a shiga Kasashen su da wannan takarda ba

– Wannan dai ba karamin tasgaro ba ne Kungiyoyi masu neman Kasar Biyafaran suka samu

Kasar Amurka sun ce ba ruwan su da wata takardar Biyafara

Kasar Amurka sun ce ba ruwan su da wata takardar Biyafara

Masu fafutukar neman Kasar Biyafara mai zaman kan ta sun ga abin kunya bayan da Kasashen Amurka da na Ingila su ka ce sam ba ruwan su da Takardun wata Kasar Biyafara. Amurka suka ce ba su san wata Biyafara ba.

Kasashen biyu sun ce babu wanda zai shigo masu Kasa da takardun Biyafara don kuwa ba Kasa ba ce mai cin gashin-kan ta. A baya dai Kungiyar MASSOB ta Biyafara tace an yarda da fasfon Kasar Biyafarar a ko ina a Duniya face Najeriya.

KU KARANTA: Turai ta sakawa Biyafara ido

Wani Babban Jami’in Kasar Amurka ya bayyana cewa Kasar sa ba ta san da wata takardar Biyafara ba. Ko da aka tuntubi takwaran sa na Kasar Birtaniya, sai yace tun zamanin Yakin basasa babu abin da ya canza, har yanzu ba su san wata Biyafara ba.

Mun yi wani rubutu inda muka nuna yanzu haka dai Manyan ‘Yan Siyasan Inyamurai irin su Orji Uzor Kalu, Ken Nnamani, Andy Uba dsr sun shiga cikin tafiyar APC. Jiya ma wata Kungiya tace idan Nnamdi Kanu zai yi kataborar sa, ya daina kiran su. Yanzu sai ka tambaya mai Inyamurai su ke so, Kasar kan su ko Shugabanci?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel