Albashin masu bautar Kasa yayi kadan-Fayose

Albashin masu bautar Kasa yayi kadan-Fayose

– Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti yace albashin masu bautar Kasa yayi masu kadan

– Fayose yace N 19,800 ba za su kai ko ina ba a halin yanzu

– Gwamna Fayose ya nemi a karawa masu bautar Kasa albashi zuwa N50000

Albashin masu bautar Kasa yayi kadan-Fayose

Albashin masu bautar Kasa yayi kadan-Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose yace albashin da ake biyan masu bautar Kasa watau NYSC yayi kadan. Gwamnan ya nemi a karawa matasan Kasar albashi don kuwa yanzu N 19, 8000 babu inda za ta.

Gwamnan ya kira Gwamnatin tarayya ta kara kudin masu bautar Kasar zuwa N50, 000. Ya kuma nemi goyon bayan Jama’a domin a samu Gwamnati ta karawa masu bautar Kasar albashin na su daga N 19 800.

KU KARANTA: Karuwa ta zama Minista a wata Kasa

A lokacin mulkin PDP ne dai watau shekaru kusan 6 da suka wuce aka kara albashin daga N9775 zuwa N19800. Sai dai fa kawo yanzu abubuwa sun canza, sun kuma kara tsada. Don hakane ake ganin kudin yayi wa masu bautar Kasar kadan.

Sai dai shi kan shi Gwamna Fayose bai biya Ma’aikatan Jihar sa albashi ba na wata-da-watanni. Jam’iyyar APC tayi ta korafin cewa Fayose ya lashe kudin da Gwamnatin tarayya ta aiko masa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel