A yiwa shugaba Buhari addu'ar samun sauki -Shugaban APGA

A yiwa shugaba Buhari addu'ar samun sauki -Shugaban APGA

Maimakon fatan mutuwa ga shugaba Buhari, an bukaci 'yan Najeriya su yi addu'a don samun sauki daga kowace irin cuta da ke damunsa

A yiwa shugaba Buhari addu'ar samun sauki -Shugaban APGA

A yiwa shugaba Buhari addu'ar samun sauki -Shugaban APGA

Chief Victor Oye, shugaban jam'iyyar APGA ne ya yi wannan kira yayin tattaunawa da 'yan jarida a jihar Anambra.

Jaridar The Guardian ta ambato Oye ya na cewa Ubangiji ya aiko Buhari a lokaci irin wannan don ya gina Najeriya kuma kawo yanzu ya yi iya kokarinsa, don haka akwai bukatar a yi masa addu'a ya dawo ya ci gaba da kyawawan ayyukan.

Da kuma ya ke magana game da zaben gwamna mai zuwa a jihar, jagoran na APGA ya ci alwashi cewa jam'iyyar sa za ta samar da gwamna a Anambra.

Yayin da ya ke nuna goyon bayansa ga gwamnati mai ci ta Willie Obiano, Oye ya dage cewa ba wata jam'iyya da za ta iya tafiyar da jihar Anambra fiye da APGA sannan ya yi alkawarin aiki da masu ruwa da tsaki da 'yan jam'iyya don tabbatar da mafarkinsu.

Ku biyo mu a Facebook a htpp://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel