Gwamna Ajimobi ya ce Najeriya ta yi sa'a da ta samu Buhari

Gwamna Ajimobi ya ce Najeriya ta yi sa'a da ta samu Buhari

- Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo ya ya yi kira ga 'yan Najeriya da su nuna jin dadinsu da zuwan Buhari

- A cewar gwamnan, ba don Buhari ya ci zaben 2015 ba, da Najeriya ta fi haka lalacewa

Gwamna Ajimobi ya ce Najeriya ta yi sa'a da ta samu Buhari

Gwamna Ajimobi ya ce Najeriya ta yi sa'a da ta samu Buhari don haka a godewa Allah

The Nation ta rawaito cewa gwamna Ajimobi ya yi wannan jawabi ne ranar Juma'a 3 ga watan Fabrairu a wajen taron shekara-shekara na hadakar cocinan Cherubim and seraphim Church of Nigeria inda mataimakinsa, Chief Moses Adeyemo ya wakilce shi.

"Nan ba da jimawa ba Najeriya za ta samu canjin da mu ke ta fata. Kasashe da dama sun shiga rudanin matsin tattalin arziki kuma sun fita har ma sun fi da karfi. Mu yi wa Najeriya addu'a kamar yadda Bible ke mana nasiha mu yi addu'a don zaman lafiya a Jerusalem.

"Najeriya ta yi sa'a da ta samu Buhari ya dare kan sirdi; ba don haka ba kalubalen da ake fuskanta yanzu da ya fi haka muni saboda cin hanci da rashawa da su ka yi katutu a gwamnatin da ta gabata. Cin hanci ya kutsa cikin duk wani fanni a kasar nan.

"Mu na kukan wahala a Najeriya saboda mutane sun daina imani da Ubangiji. Da za mu yi mu'amala kamar yadda mu ke bautawa Ubangiji a coci da masallatai, to da Najeriya ta yi kyau.''

'Yan Najeriya sun kwashe kayansu daga gaban Ubangiji.

Bible ba ya koya mana kashe ran da bai ji ba bai gani ba da sace dukiya da wasu tsiraru ke yi don amfanin kansu da 'ya'yansu da za a haifa. Mu dawo da mutunta mutane mu kuma so makwabtanmu," kamar yadda aka ambato shi ya na fada.

Ajimobi ya kuma musanta rahotannin da ke cewa an gayyace shi shi da wasu gwamnoni zuwa taron gaggawa a Abuja don tattaunawa game da lafiyar shugaba Buhari.

The Guardian ta rawaito cewa Ajimobi ya fada a Ibadan ranar Lahadi 29 ga watan Janairu cewa babu kamshin gaskiya a zancen.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel