Tarayyar Turai ta ba mas son kafa Biafara amsa

Tarayyar Turai ta ba mas son kafa Biafara amsa

- Tarayyar Turai ta ba kungiyar fafutukar kafa kasar Biafara IPOB amsa kan bukatarsu na ballewa daga Najeriya

- Kungiyar ta Tarayyar Turai ta hannun kungiyar OEAS da masu neman kasar Biafara cewa neman 'yanci da canje-canje a kan iyaka dole ne a yi su bisa tanade-tanaden dokokin kasa da kasa

Tarayyar Turai ta ba masu kiraye-kirayen kafa kasar Biafara amsa

Tarayyar Turai ta ba masu kiraye-kirayen kafa kasar Biafara amsa

A game da kiraye-kirayen masu neman samar da kasar Biafara da kungiyar kula da kasashen Africa masu kokarinn kafa kansu a karkashin Tarayyar Turai nakada kuri'ar jin ra'ayinmu jama'a kan samun 'yancin jamhuriyar Biafara, Kungiyar tarayyar Turai ta bada amsa ga masu kokarin tabbatar da kasar ta Biafara.

Kungiyar 'yan IPOB masu fautukar kafa kasar Biafara sun roki babban wakilin Tarayyar Turai EU kan harkokin kasashen waje da tsaro, Federica Mogherini ya sa baki game da bukatar kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da 'yancin kasar Biafara. An yi kiran ne ta hanyar kungiyar ta OEAS.

Kungiyar ta kuma yi Kira da a saki wadanda ta kira da 'fursunonin siyasar Biafara' da fadan da sojojin Najeriya su ke yi da kuma gaggauta kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a cikin kwana 90.

Da ya ke ba da amsa ga wannan rokon, Mogherini ya fadawa Dr. Jonathan Levy, wanda shi ne shugaban OEAS cewa, duk da kungiyar ta Tarayyar Turai tana da kyakkyawar huldar diflomasiyya da alakar tattalin arziki da Najeriya, kare hakkin dan adam da 'yanci su, kungiyar ta fi ba wa muhimmanci kuma muna karfafar Najeriya ta kare wadannan hakkoki ta ko wane yanayi.

Kungiyar ta Tarayyar Turai ta gargadi OEAS da masu neman kasar Biafara cewa neman 'yanci da canje-canje a kan iyaka dole ne a yi su bisa tanade-tanaden dokokin kasa da kasa.

Ta kara da cewa kasar ta Biafara za ta karbu ne kadai ta hanyar dokokin kasa da kasa ba ta hanyar tawaye ba.

OEAS ta dade tana neman a gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a karbabbiya a idanun duniya game da samun 'yancin Biafara.

Haka kuma, OEAS ta bada shawara cewa a bi duk wata hanya da ba ta tashin hankali ba wadda ta hada da yajin aiki da kauracewa harkokin tattalin arziki da zanga-zanga da tafiya gaban kuliya da bijirewa gwamnati.

Kungiyar Kwadago ta kasa da kasa ILO a takaice ta amince da damar shiga yajin aiki sannan tanade-tanaden kungiyar kasa da kasa kan hakkokin tattalin arziki da na zamantkewa da al'adu na shekarar 1966 (Article 8(1)(d)).

sun amince da damar shiga yajin aiki. Kuma Najeriya mamba ce a kungiyar Kwadago ta kasa da kasa ILO.

Ku biyo mu a Facebook a htpp://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel