DSS ta saki tsohon gwamna Ibori

DSS ta saki tsohon gwamna Ibori

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sallami tsohon gwamna James Ibori bayan ganawarsa da shugaban hukumar na wani dan kankanin lokaci

DSS ta saki tsohon gwamna Ibori

DSS ta saki tsohon gwamna Ibori

A yau ne James Ibori ke dawowa Najeriya bayan kammaala wa'adin da zaman gidan yari na shekaru 13 a Biritaniya.

Tsohon gwamnan jihar Delta Jame Ibori ya nufi gida bayan ganawarsa da shugaban Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS.

Ibori wanda ya dawo gida Najeriya bayan a ranar Asabar 4 ga watan Fabarairu shekarar 2017 bayan kammaala wa'adin zaman gidan yari na shakaru 13 da wata kotun Ingila ta daure shi bayan ta same shi da laifi.

Jami'an hukumar dai sun yi awon gaba da shi ne zuwa babban ofishinsu a lokacin da ya sauka a kasar domin abin da suka kira wata 'yar tattaunawa.

Rahotanni na cewa, tsohon gwamnan a tuni ya kama hanyar zuwa mahaifarsa Oghara a inda 'yan uwa da abokan arziki suka shirya masa wata gagarumar tarba.

James Ibori wanda ya taba rike mukamin gwamna a jihar Delta mai arzikin Mai, an sako shi ne daga kurkuku a watan Disambar shekarar 2016 bayan ya kammala wa'adinsa na zaman gidan yari da wata kotun Birtaniya ta yanke masa hukunci.

Jim kadan bayan sakinsa Ibori ya yi alkawarin dawowa Najeriya domin ya cigaba harkokin siyasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel