Kafa kwamitin rage farashin kayan abinci ihu ne bayan hari - Majalisar wakillai

Kafa kwamitin rage farashin kayan abinci ihu ne bayan hari - Majalisar wakillai

- Gwamnatin tarayyar Najeriya da Muhammadu Buhari ke jagoranta ta kafa wani kwamitin manyan ministoci domin ya samo mata hanyar rage farashin kayan abinci a duk fadin kasar

- Ko shakka babu hau-hawan farashin abinci da na kayan masarufi ya zama wa 'yan Najeriya alakakai

Kafa kwamitin rage farashin kayan abinci ihu ne bayan hari - Majalisar wakillai

Kafa kwamitin rage farashin kayan abinci ihu ne bayan hari - Majalisar wakillai

Kwamitin da ya kunshi ministocin sufuri da noma da albarkatun kasa da kudi da dai sauransu an bashi mako daya ya ba gwamnatin tarayya rahoto.

Sai dai dan majalisar wakillai Alhaji Alhassan Ado Doguwa wanda kuma shine mai tsawatawa na zauren majalisar ya ce kafa kwamitin ya zo daidai da abun da ake kira ihu bayan hari.

Ya ce a tsari irin na dimokradiya dole sai gwamnati ta yi wani tanadi domin a yi maganin abun dake faruwa inda ya ce kwamitin an kafashi a lokacin da za'a ce an makara.

Hon. Ado ya ce idan gwamnati ta na son ta shigo harkar rage kudin abinci dole ne a ce ta yi tanadi a cikin kasafin kudi domin lamari ne da zai bukaci kudin gwamnati bayan da kwamitin ya mika rahotonsa.

Sai dai ya ce a cikin kasafin kudin da gwamnati ta gabatar babu abun da ya yi kama da wannan rage kudin abinci.

Wani manomi Musa Labaran ya ce aikin kwamitin ba zai yi tasiri ba idan ba an kawowa manoma sauki akan kayan aikin noma ba babu yadda farashi zai ragu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota
NAIJ.com
Mailfire view pixel