Nima so 12 ana kashe ni - Obasanjo

Nima so 12 ana kashe ni - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana masu yada jita-jita cewa shugaba Buhari ya mutu a matsayin macuta, marasa imani sannan kuma marasa hankali.

- Shugaba Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da mai kula da harkokin yada labaran shi ta fitar daga hannun Kehinde Akinyemi a garin Abeokuta a jiya.

Nima so 12 ana kashe ni - Obasanjo

Nima so 12 ana kashe ni - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana masu yada jita-jita cewa shugaba Buhari ya mutu a matsayin macuta, marasa imani sannan kuma marasa hankali.

Shugaba Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da mai kula da harkokin yada labaran shi ta fitar daga hannun Kehinde Akinyemi a garin Abeokuta a jiya.

Obasanjo ya cigaba da cewa kamata yayi yan Najeriya su dukufa wajen yi ma shugaba Buhari addu'o'I don samun lafiyar sa tare da dawowar sa don ci gaba da mulkar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin dan Bala Mohammed kan naira 100m

Obasanjo ya kuma gargadi masu anfani da sunan siyasa wajen jefa kasar nan cikin rudani inda kuma ya bayyana kansa a matsayin wanda ya sha irin wadannan rade-raden na mutuwa a lokacin mulkin sa.

A cewar sa: "Babu wani mai hankalin da zai yi addu'ar wani duk da ko wane irin bambancin dake tsakanin su. Idan baka son shi to ka jira zabe ya sake zagayowa sai ka sake zabar wani wanda kake ganin ya fi shi. A gani na duk wanda yake yada jita-jitar ya mutu to gaskiya bai da hankali da tunani."

"Nima a lokacin mulki na so 12 ana cewa na mutu. So 12 wasu na kashe ni. Ban san me yasa suke jin dadin fadin hakan ba amma ya kamata su roki gafara. Ko da shugaba Buhari baya lafiya kamata yayi ayi mishi addu'a ba fatan mutuwa ba. Bai kamata mu rika saka siyasa cikin komai ba. Ya kamata mu rika girmama manyan mu a Najeriya." Yace.

Wani bangare ne dai na kafofin yada labarai yayi ta yada cewa shugaba Buhari ya mutu a kasar Landan a satin da ya gabata inda yaje hutun kwanaki 10.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel