Kotun Amurka ta dakatar da dokar Trump na hana musulmai shiga kasar

Kotun Amurka ta dakatar da dokar Trump na hana musulmai shiga kasar

A wani mataki na wucin gadi, wata kotu a Amurka, ta dakatar da shugaba Donald Trump haramtawa 'yan kasashe bakwai da musulmai suka fi yawa shiga kasar.

Hukumar shige da ficen Amurka, ta shaidawa kamfanonin jiragen sama su koma bakin aikinsu, tare da ci gaba da dauko fasinjojin kasashen da mista Trump ya sanya hannu kan a hana su shiga kasar a makon da ya wuce.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin dan Bala Mohammed kan naira 100m

A wani yunkuri na kalubalantar gwamnati, alkalin kotun ya ce matakin da gwamnatin mista Trump ta dauka sam ya sabawa kundin tsarin mulkin Amurka, wanda ya haramta fifita wani addini ko maida masu bin wani addini saniyar ware.

Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke nuna cewa shugaban kasar Donald Trump na nuna zai cika alkawarin da ya dauka wa Amurkawa a lokacin yakin neman zabe.

To sai dai yanzu haka ta na kasa ta dabo, tsakanin alkalan kasar da kuma bangaren gwamnati.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel