Dandazon matasa ne za su tarbi Buhari

Dandazon matasa ne za su tarbi Buhari

- Majalisar matasa na gangamin matasa sama da 1,500 domin su tarbi shugaba Buhari a yayin dawowarsa daga Birtaniya

- Ana yin hakan ne a daidai lokacin da fitaccen mawaki 2baba ke shirin gudanar da zanga-zangar adawa ga shugaban a ranar dawowarsa

Dandazon matasa ne za su tarbi Buhari

Mawaki 2baba ne ya shirya zanga-zangar adawa da gwamnatin Buhari da ya sa majalisar matasa in karinsa da matasa 1,000

Ana sa ran matasa kimanin 1,500 ne za su yiwa shugaba Buhari marhabin idan ya sauka da daga birnin Landan bayan karewar hutunsa na kwanaki 10.

Hakan a matsayin inkari ne ga zanga-zangar da wani shahararren mawaki 2baba ya shirya jagoranta na nuna adawa ga gwamnatin ta Buhari.

Majalisar Matasan Najeriya ce ta shirya dandazon matasa kimanin 1,500 wadanda su kuma za tarbi shugaban kasar idan ya dawo a ranar Laraba 6 ga watan Fabarairu a babban birnin tarayya Abuja.

Malam Gambo Jagindi jam'i mai ba da shawara na musamman kan harkakokin yada labarai ga Majalisar, ya kuma yi kira ga matasa wadanda su ne manyan gobe da fito su nuna kauna ga shugaban a ranar da zai dawo Najeriya daga Ingila

Ya kuma ce, "kowa dai yana ganin yadda shugaban ke kokarin dawo da da'a, da nagarta da kuma gaskiya da rikon amana a kasar nan, ba kamar a baya ba, don aka ya kamata mu fito mu nuna goyon bayanmu ga shugaban da ya ke yi mana wannan gatan".

Shugaban matasan ya kuma yi tir da wadanda ke yada jita-jitan mutuwar shugaban yana mai kiransu da cewa, bata gari ne wadanda ba sa son cigaban Najeria.

Ku biyo mu a http://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel