APC ta yi hasarar magoya baya a Katsina

APC ta yi hasarar magoya baya a Katsina

- Wadanda suka canza shekar sun yi zargin rashin aldalci a APC wanda ya sa hakan suka yanke shawarar barinta

- Shugaban PDP a jihar ya ce, sun kafa kwamitin karbar wadanda suka koma jam'iyyar daga sauran jam'iyyu

APC ta yi hasarar magoya baya a Katsina

Magoyan bayan jam'iyyar APC mai mulki kimanin 1,500 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina.

A rahoton da Jaridar Vangurad ta bayar ta ce, yawancin wadanda suka sauya shekar daga garin Randa suke na karamar hakumar Chiranci ta jihar Katsina, sun kuma sauya shekar ne a ranar Juma'a 3 ga watan Fabarairu shekarar 2017.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

Shugaban jam'iyyar PDP Salisu Majigiri ne ya tabbatar da labarin komawar 'yan jam'iyyar APC, ya kuma kara da cewa, suna kokarin kafa wani kwamitin mai karfi da zai karbi wandanda suka koma jam'iyyar.

Cikin wadanda suka sheka zuwa PDP a jihar, sun hada wani jigon jama'iyyar APC Mustapha Radda, wanda kuma shugaban jam'iyyar ne a Randa, kuma ya taba rike mukamin jami'in gangamin matasa na jihar Katsina daga shekara 2010 zuwa 2016.

Har yanzu dai ba 'a ji ta bakin jam'iyyar APC ba kan lamarin

Ku cigaba da bin mu a http://www.facebook.com/naijjcomhausa ko a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel