Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

Ga bitar wasu manyan labarai 4 da muka kawo muku a jiya Juma'a 3 ga watan Fabarairu a 2017 ga wanda bai samu daman karantawa ba.a

1. Obasanjo ya gargadi 'yan Najeriya kan shugaba Buhari

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan rade-radon mutuwar shugaba Buhari da wasu 'yan Najeriya ke yi da cewa wannan abin Allah wadai ne.

Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

2. An gano jini da kokon kan mutum a wani coci a jihar Imo

hankula sun tashi a kauyen Ububo-Alia, Awara da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo a inda aka gano kokon kan mutane 5 cikin wani coci da ake kirra Ark of covenant.

Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

3. Jonathan ya yafewa wani wanda ya zargi shi da ruguza Najeriya

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yafewa wani wanda ya zarge shi da rugurguza Najeriya a shekarar 2014. Jonathan ya bayyana hakan ne ta hanyar wani sako da ya lika shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis 2 ga watan Fabarairu shakarar 2017.

Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

4. Buhari na nan da ransa sai dai yana bukatar addu'a

Ministan Sadarwa Adebayo Shitu ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa, Shugaba Buhari na nan da ransa. A rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, Minista Shittu ya yi watsi da rade-radin da ake yi na mutuwar shugaban, ya kuma ce ba abin da ya ke bukata illa addu'a domin cin gaba da ayyukan alheri a kasar.

Waiwaye: Manyan Labarai 4 na juma'a

Ku cigaba da bin mu a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naicomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel