Wata ýar koyan aiki tayi basaja ta sace ýar uwarɗakinta

Wata ýar koyan aiki tayi basaja ta sace ýar uwarɗakinta

Wata budurwa da ta badda kama a zuwan ita yar koyan aiki ce, Grace John ta sace yarinyar uwardakinta Oluwasemilore Adebiyi mai shekaru 3 a ranar Asabar 28 ga watan Janairu.

Wata ýar koyan aiki tayi basaja ta sace ýar uwarɗakinta

Wata ýar koyan aiki tayi basaja ta sace ýar uwarɗakinta

Uwar yarinyar, Tobilola Adebiyi tana da shagon hada murjani a shago mai lamba 1 a kan titin James Oyedele a yankin Alagbado na jihar Legas.

Wanda ake zargi da satar yarinyar, yar aiki Grace John ta fara koyan aiki ne a ranar Litinin 23 ga watan Janairu, inda mai shagon ta bukaci ta kawo mutanen da zasu tsaya mata, amma ta dinga yi mata wala wala.

KU KARANTA: Miji, mata da ýaýansu 3 sun rasu a haɗarin mota

Mahaifin karamar yarinyar yace: “A ranar wata Asabar 28 ga watan Janairu ne Grace ta fada ma matata wai zata je ta siyo gala, a nan ne fa yarinya tat a roki matata data kyale tat a raka Grace. Sai matar tawa ta yarje ma yarinyar mu ta bita.

“Amma bayan kwashe sa’o’i kadan da tafiyar Grace da yarinyar mu amma basu dawo ba, shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu. Daga nan ne fa matata ta shiga nemanta, can sai ta hange su tare da wani mutum, inda yace mata wai dama shagonta zai zo don ya gabatar da kansa a matsayin yayan Grace.

“Daga nan sai matata ta rabu dasu, tsammaninta zasu biyo ta shagon, amma shiru kake ji, koda tabi sahu, sai ta nemi su a inda ta barsu ta rasa. Daga nan ne fat a fara kiran lambar Grace, amma ta kashe wayar.”

Mahaifiyar yarinyar tace ta dauki hoton yar aikin nata Grace John, amma tun bayan faruwar lamarin bata sake ganin hoton a wayanta ba. Don haka take rokon jama’a cewa duk wanda ya san inda yarinyar take ya sanar dasu ta wannan lambar 08028521316.

Mu dai a nan sai muce Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel