Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Majalisar dattawa ta kaddamar da fara shirye shiryen yi ma dokokin hukumar kwastam garanbawul don hana wani bare daga waje sake zama shugaban hukumar a nan gaba.

Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Shugaban kwamitin hukumar kwastam na majalisar dattawa Sanata Hope Uzodinma (PDP, Imo) ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da tsofaffin shuwagabannin kwastam su biyar a kokarin majalisar na yi ma dokokin hukumar kwastam garambawul.

KU KARANTA: Miji, mata da ýaýansu 3 sun rasu a haɗarin mota

Uzodinma yace za’a kafa ma hukumar kwastam cibiya, wanda zata maye gurbin majalisar koli ta hukumar, inda yace idan an kafa cibiyar, za’a zabo daya daga cikin tsoffin shuwagabannin hukumar don ya jagoranci cibiyar.

Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Sanata Hope Uzodinma shugaba kwamitin kula da huukumar kwastam na majalisar dattawa

Sabuwar cibiyar da zamu kirkiro zata sanya idanu akan al’ummar hukumar yaki da fasa kauri, sa’annan kuma zata maye majalisar koli ta hukumar. Ba zamu yadda da nadin bare daga waje a jagorantar hukumar kwastam ba, saboda haka ne ke rage ma kasa kudaden shiga.” Inji Sanata Uzodinma.

Yayin dayake bukatar shawarwari da hadin kai daga tsofaffin shuwagabannin hukumar, inda yace sabuwar cibiyar da za’a kirkiro zata taimaka wajen habbaka kudaden shigan kasar nan.

Daga cikin tsofaffin shuwagabannin da suka halarci taron sun hada da Bello Haliru, Jacob Gyang Buba (Gbong Gwon Jos), Nwadialo Benard-Shaw, A. Mustapha da A Kajoli. Shima Bello Halliru ya bukaci a cigaba da horar da jami’an hukumar don tabbatar da ingantaccen aiki.

Bello Halliru ya kara da cewar “kamata yayi a kira shugaban hukumar kwastam mai ci da sunan mukamin shugaban-riko, don haka dole a yi gyare gyare don karfafa hukumar.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel