An damke kwamandan Boko Haram da ya kai hari kasuwan Adamawa

An damke kwamandan Boko Haram da ya kai hari kasuwan Adamawa

Rahoto ya nuna cewa babban dan Boko Haram din da ya kai hari wata kasuwa a Madagali, jihar Adamawa, a watan Disamban 2016 ya shiga hannun hukuma.

An damke kwamandan Boko Haram da ya kai hari kasuwan Adamawa

An damke kwamandan Boko Haram da ya kai hari kasuwan Adamawa

Rundunar sojin Najeriya tare da hadin kan wasu hukumomin tsaro na samun nasara wajen kokarin dakile ta’addanci a Najeriya.

Dan Boko Haram din mai suna Ibrahim, wanda aka damke a ranan 20 ga watan Junairu ya bayyana cewa lallai ya taka rawan gani a harin da aka kai wata kasuwa ranan Juma’a,9 ga watan Disamba,2019, inda aka rasa akalla rayuka 30.

KU KARANTA: Kato yayiwa yarinya fyade a Gombe

Jaridar Daily Times ta bada rahoton cewa hukumar yan sanda ta damke shi ne tare da gudunmuwan rundunar sojin Najeriya a wata aikin duba-duben hanya a ranan 20 ga watan Junairu,2017.

Kwamandan tiyatan rundunar sojin Operation Lafiya Dole ya tabbatar da wannan kamu kuma yace dan Boko Haram din na bada hadin kai ga jami’an tsaro.

Kana kuma, rahoton tace an damke wani abun zargi, dan kasar Mali mai suna Ayuba wanda ake zargin na taimakawa yan ta’a dda.

“A ranan 20 ga watan Junairu, tare da hadin kan hukumar yan sanda a jihar Gombe, an gudanar da wata farmaki bisa ga labarin liken asirin da aka samu.

“An damke wani dan Boko Haram mai suna Ibrahim. Yayinda ake tambayarsa, ya bayyana cewa yanada hannu cikin harin Madagali.

“Kana kuma yace yaje garin Chibok domin kai hari. Yanzu yana hannun jami’an tsaro yana amsa tamabayoyi.

“Kana kuma akwai wani dan kasar Mali, wanda yaren faransa kawai ya iya. Amma bisa ga masi mana fassara, shima ana bincikensa a matsayin dan Boko Haram.”

A bangare guda, rundunar soji ta kwace wasu manyan makamai daga hannun yan Boko Haram a kwanakin da ya gabata.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel