Kamaru kai wasan karshe bayan ta fidda Ghana a gasar cin kofin Afrika

Kamaru kai wasan karshe bayan ta fidda Ghana a gasar cin kofin Afrika

- Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta fitar da Ghana daga gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Gabon bayan sun tashi wasa da ci 2-0 a fafatawarsu ta jiya a birnin Franceville.

- Kamaru ta samu nasarar zura kwallayen ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, in da Michael Ngadeu-Ngadjui ya zura kwallon farko a minti na 72, yayin da Christian Bassogog ya zura ta biyu a minti na 93.

Kamaru kai wasan karshe bayan ta fidda Ghana a gasar cin kofin Afrika

Kamaru kai wasan karshe bayan ta fidda Ghana a gasar cin kofin Afrika

A ranar Lahadi mai zuwa ne Kamaru za ta kara da Masar a matakin wasan karshe na wannan gasar ta cin kofin Afrika wadda ita ce, karo na 31.

Kocin Kamaru Hugo Broos ya ce, burinsu na zuwa matakin wasan karshe ya cika duk da cewa, Ghana ta fi su kwarewa wajen murza tamaula.

A wani labarin kuma, Barcelona ta doke Atletico Madrid a karawarsu ta farko ta wasan kusa da na karshe na cin kofin Copa del Rey a gidan 'yan Madrid din Vicente Calderon.

Luis Suarez ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na bakwai da shiga fili, sannan kuma Lionel Messi ya kara ta biyu a minti na 33.

Sai dai Antoine Griezmann ya ba wa masu masaukin bakin kwarin guiwa a karo na biyu da za su yi a ranar Talata a Nou Camp, sakamakon kwallo daya da ya rama a minti na 59, wadda ya ci da kai.

Alaves da Celta Vigo su ne sauran kungiyoyin da suka kai wasan na kusa da karshe, inda za su yi wasansu na farko ranar Alhamis.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel