An kama wani mutumi a Lagas kan daure abokin aikinsa bayan mota zuwa Abuja (HOTO)

An kama wani mutumi a Lagas kan daure abokin aikinsa bayan mota zuwa Abuja (HOTO)

Yan sanda sun kama wani injiniya Odunuga a hanyar Ketu/Ojota jihar Lagas kan daure hanneye da kafafun wani mutumi da aka kira da Daniel Dabis, a bayan motar sa ta Hilux.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Odunuga yayi ikirarin cewa mutumin da ya daure a bayan motarsa ya sace mai kudi ne a gidansa dake Abuja sannan ya gudu zuwa jihar Lagas. Ya kara da cewa, zai kai Debis, wanda ya bayyana a matsayin mataimakinsa a ofis, zuwa Abuja ne lokacin da yan sanda suka tsare shi.

An kama wani mutumi a Lagas kan daure abokin aikinsa bayan mota zuwa Abuja (HOTO)

Daniel Dabis da aka daure cikin motar Hilux

Odunuga yace: “Ina ta neman sa a ko ina. Neman nasa ya kaini har kauyensa a jihar Plateau. Wani daga cikin abokansa ne ya fada mun cewa yana jihar Lagas inda ya boye. A take, aka sanar dani cewa yana zama ne a kasuwar Mile 12, Ketu. Na tashi daga Abuja na kuma same shi a kaswar Mile 12 Ketu inda na kamo shi. Da farki na dauke shi zuwa ofishin yan sandan Ketu jihar Lagas don na yi karan al’amarin, amma jami’an yan sandan suka ki tsare shi a na. don haka bani da wani zabi da ya wuce na mayar dashi Abuja. Abunda nake shirin yi kenan da yan sanda suka tsare ni a hanya.”

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Da yake kare kansa, Dabis ya bayyana cewa abunda ya dauka daga Odunga ba komai bane face tsauni da amalanke kuma ba don yan sanda sun shigo lamarin ba da ya kashe shi.

Yace: “Abunda satar mai ya kasance tsauni da wani amalanke. Ya kayyade farashin amalaken a matsayin naira dubu dari da goma (N110,000) da kuma tsaunin N90,000 shikenan abunda na satar masa.saboda haka ne ya daure mun kafa da hannaye zuwa bayana. Shirin sa shine ya kaini Abuja. Ba don jami’an yan sandan ba, da kashe ni ya ajiye gawana a kan hanya.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel