Ba zamu bari ayi wa Buhari zanga-zanga ba - 'Yan sanda

Ba zamu bari ayi wa Buhari zanga-zanga ba - 'Yan sanda

- Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Legas Fatai Owoseni ya ce, ba zasu bada damar yin zanga zangar da aka shirya gudanarwa a jihar ba, kan halin matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta

- A ranar Talatar da ta gabata, daya daga cikin shahararrun mawaka a Najeriya, 2Face Idibia, ta shafinsa na Twitter, ya bukaci masoyansa su fito don yin zanga zangar, a ranar 5 ga watan da muke ciki

Ba zamu bari ayi wa Buhari zanga-zanga ba - 'Yan sanda

Ba zamu bari ayi wa Buhari zanga-zanga ba - 'Yan sanda

Sai dai Kwamshinan ‘yan sandan jihar Legas, Fatai Owseni, ya ce babu wata bukata ko neman izinin gudanar da wannan zanga zanga da wadanda ki shirin gudanar da ita suka gabatar.

Zalika Owseni ya ce suna da rahotanni na sirri da ke nuna cewa, wasu bata gari, suna yunkurin yin amfani da damar gudanar da zanga zangar, wajen tada zaune tsaye.

A jiya ne dai muka wallafa cewa Fitaccen mawakin Najeriya 2face Idibia ya yi kira ga masoyan shi su fito zanga-zanga a ranar Talatar makon gobe domin adawa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Zalika mawakin ya bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan magance matsalar.

2face ya yi kiran ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin shi na facebook, wanda kuma cikin sa’a guda, sama da mutane dubu ashirin da biyu suka kalli sakon.

Kafofin sadarwa na intanet dai sun kasance hanyoyin kiran gangamin zanga-zanga a Afrika, to sai dai kuma abin mamaki ne mawaki ya fito ya dauki irin wannan matsayin na siyasa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel