To fa! Wani Mahauci yayi ma wata yarinya fyade a Gombe

To fa! Wani Mahauci yayi ma wata yarinya fyade a Gombe

- Kotu a jihar Gombe ta gurfanar da wani mahauci dan shekara 25 mai suna Shamsudeen Musa da laifin yi ma wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.

- Alkalin kotun mai shari’a Bello Sheriff ranar Alhamis ya bada umurin a cigaba da ajiye Shamsudeen a kurkukun Zirindaza akan laifin da yayi zuwa 1 ga watan Maris.

To fa! Wani Mahauci yayi ma wata yarinya fyade a Gombe

To fa! Wani Mahauci yayi ma wata yarinya fyade a Gombe

Ismail Adamu wanda shine ya kai Shamsudden kara ya shaida wa kotu cewa mahaucin ya aikata laifin ne ranar 20 ga watan Janairu da karfe 12:30 na rana.

Ismail ya ce mahaucin ya rudi yariyar ne zuwa wani kangon gini inda ya danne ta da karfin tsiya ya yi mata fyaden.

Ya roki alfarmar kotu da ta daga shari’ar har sai bayan ‘yan sanda sun gama bincike.

A wani labarin kuma, farkon satin nan wata kotun soja a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno ta yankewa wasu sojoji biyu hukuncin dauri saboda ta samesu da laifuka da aka zargesu da aikatawa.

Birgediya Janar Olusegun Adeniyi shi ne shugaban kotun wanda ya yanke ma sojojin biyu hukuncin dauri a gidan kaso.

Kotun ta yankewa Hassan Adamu hukuncin shekaru bakwai a gidan kaso sakamakon laifin kisa da aka sameshi dashi amma kuma ba da gangan ba. An zargeshi da aikata laifin ne ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2015 sakamakon durkawa wani Umar Aka harsashai har sau biyu a kirjinsa a bakin kasuwar Litinin ko Monday Market. Nan take Umar Aka ya bar duniya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel