CANJI! Buhari zai kara siyo karin wani jirgin kasa

CANJI! Buhari zai kara siyo karin wani jirgin kasa

- Gwamnatin Najeriya ta amince da a karo sababbin taragon jirgen kasa domin jigilan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja.

- Ministan Sufuri, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan wa manema labarai a fadar gwamnati dake Abuja.

CANJI! Buhari zai kara siyo karin wani jirgin kasa

CANJI! Buhari zai kara siyo karin wani jirgin kasa

Ministan yace gwamnati tayi hakanne ganin yadda matafiya zasu karu musamman daga Kaduna zuwa Abuja nan da wata mai zuwa a dalilin gyaran filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja da za’a fara.

Filin jirgin saman Kaduna ne za’a yi amfani dashi domin hada-hadan jiragen sama wanda hakan yasa za’a samu Karin yawan mutanen da zasu dinga bin hanyar daga Kaduna zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Kwanakin baya gwamnati ta bada kwangilan gyaran hanyar Kaduna zuwa Abuja duk saboda hakan.

A wani labarin kuma, Fitaccen mawakin Najeriya 2face Idibia ya yi kira ga masoyan shi su fito zanga-zanga a ranar Talatar makon gobe domin adawa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Zalika mawakin ya bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan magance matsalar.

2face ya yi kiran ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin shi na facebook, wanda kuma cikin sa’a guda, sama da mutane dubu ashirin da biyu suka kalli sakon.

Kafofin sadarwa na intanet dai sun kasance hanyoyin kiran gangamin zanga-zanga a Afrika, to sai dai kuma abin mamaki ne mawaki ya fito ya dauki irin wannan matsayin na siyasa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel