Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Ganawar da gudana tsakanin shugaban kasa mai rikon kwarya Yemi Osinbajo da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu na da alaka da kare kasafin kudin 2017, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Saraki ne ya bayyana hakan a wani hira tare da yan majalisa jim kadan bayan ganawar.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa shi da kakakin majalisa Yakubu Dogara ne suka halarci taron, kuma an basu tsokaci kan halin da sojojin Najeriya ke ciki a kasar Gambia.

KU KARANTA KUMA: Munyi alkawarin canji kuma yazo – Lai Mohammed

Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

“Shugaban kasar mai rikon kwarya ya bamu tsokaci a kan rundunarmu dake kasar Gambia kuma da halin da ake ciki. Kuma cewa sojin saman da ruwan zasu dawo nan ba da jimawa ba. Kuma akwai yiwuwar barin wasu runduna a chan,” cewar sa.

Ku tuna cewa taron jiya ya zamo karo na biyu da Bukola ya gana tare da Osinbajo a wannan makon, yayinda ya kasance karo na uku da Dogara ya gana da shugaban kasar mai rikon kwarya a wannan makon.

Na farko da Dogara ya gana dashi ya kasance a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci tare da Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo.

A ranar Talata, 31 ga watan Janairu, shugaban majalisar dattawa ya ziyarci Villa tare da shi kuma.

Osinbajo ya zama shugaban kasa mai rikon kwarya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke hutu a birnin Landan ya mika masa mulki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel