Kudancin Kaduna: An kama wasu da manyan makamai

Kudancin Kaduna: An kama wasu da manyan makamai

– Jami’an ‘Yan Sanda sun damke wasu daga cikin masu tada rikici a Kudancin Kaduna

– Yanzu haka an kama mutane kusan 17 wanda suna hannun Hukuma

– Za a gurfanar da masu laifin a Kotu

Kudancin Kaduna: An kama wasu da manyan makamai

Kudancin Kaduna: An kama wasu da manyan makamai

Hukumar ‘Yan Sanda ta samu nasarar damke wasu daga cikin masu hannu a rikicin Kudancin Kaduna. ‘Yan Sanda dai sun kama mutane 17 da manyan makamai kamar kuma tuni za a wuce da su Kotu bayan an gama tsare su.

Kakakin ‘Yan Sanda na Kasa, Jimoh Mashood yace Hukumar tayi nasarar kama wadanda ake zargi, ta kuma tsare su inda tayi masu tambayoyi, ana kuma kammala bincike za a maka su a gaban Kotu kamar yadda Premium Times ta bayyana.

KU KARANTA: An kama wani babban dan ta'adda a Najeriya

Sunayen wadanda aka kama sun hada da: Magaji Shu’aibu, Abdulkareem Abdul, Goma Adamu, Danlami Yakubu, Danjuma Barde, Idris Bello, Adamu Haruna, Suleiman Saleh, Adamu Umar, Abubakar Muhammad, Bulus Jatau, Nelson Paul, Hassan Idris, da sauran su.

Jami’in ‘Yan Sandan yace za a gurfanar da su da laifin daukar makamin da bai hallata ba, tada zaune-tsaye da ma sata. An dai same su da manyan makamai kusan 29.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel