Rundunar sojojin Najeriya ta saki jerin daukar ma'aikata na 2016

Rundunar sojojin Najeriya ta saki jerin daukar ma'aikata na 2016

Rundunar sojojin Nijeriya ta fito da jerin sunayen mutane 76 a wata sakamakon tatancewar sa.

Rundunar sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Nijeriya a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu ta fito da wani jerin sunaye 76 na wayanda suka ci nasara a daukar ma'aikata na 2016.

A cikin wata sanarwar da shugaban gudanar da hayyukan sojojin Najeriya M.I Alkali ya sanya hannun, ya ce, za a iya samu sakamakon tantancewar a shafin yanar gizo www.narecruitment.org.

Alkali, wanda kuma Manjo Janar ne ya ce an gudanar da tantancewar da kuma jarrabawa a watan Janairu 7, 2017.

Alkali ya ce: "Rundunar sojojin najeriya ya na mai sanar da jama'a cewa sakamakon tantancewa na rukuni 76 na jerin daukar ma’aikata wanda aka gudanar a ranar Asabar 7 ga watan Janairu 2017, ya fito kuma za a iya samu a shafin yanar gizo www.narecruitment.org na rundunar.”

Manjo Janar ya shawarci dukan 'yan neman shiga su duba shafin yanar gizon rundunar kuma su tabbatar da cewa sun buga shafin da ke nuna tabbacin cin nasara..

Rundunar ta ce wayan da suka buga wannan shafin ne kawai za a ba damman shiga zaman tatancewa a shiyyoyin gudanar da zamman tsakanin watan Fabrairu 19 zuwa Maris 3.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar 'yan na tsaya tare da Buhari za ta kaddamar da gangamin taro na kasa

Alkali ya kuma ce: "Wayan da suka ci nasara a zabin na farko sa su hallara wurin tantancewa na shiyyoyi a jihohin su.''

Wayan da suka ci nasara bayan tantancewar shiyyoyi za a fara horad da su nan da nan a daffo rundunar sojojin Najeriya ta Zaria.

Alkali ya shawarce su cewa su zo tare da farin falmaran guda biyu, gajeren wando biyu mai kalar shude, ainihin takardun shaida da kuma kwafa, kayan rubutu, farin canvas da farin safa.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel